Pate ya zabi Gwadabe a matsayin mataimaki


Dantakarar gwamnan jihar Bauchi a karkashin jam’iyar PRP, Farfesa Muhammad Ali Pate ya zabi Barista Ahmad Faruk Gwadabe a matsayin wanda zai masa mataimaki.

Farfesa Pate ya yi alkawarin cewa idan aka zabe shi, gwamnatinsa zata yaki matsanancin talauci ta hanyar ɓullo da sabbin hanyoyi da su kara kudaden da magidanta ke samu.

Dan takarar ya kara da cewa za su kafa kanana da kuma manyan sansanin masanantu a kowace shiya dake jihar.

Ya ce za kuma su hada kai da kamfanoni na gida dana ƙasashen waje domin samar da abubuwan more rayuwa kamar su hanyoyi, ruwan sha da kuma gidaje.

Har ila yau dantakarar gwamnan a jam’iyar ta PRP ya ce za su bada tallafin kudi dama na kuɗin karatu ga dalibai masu hazaka da iyayensu basu da karfi.


Like it? Share with your friends!

0

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like