Pantami Zai Maka Wadanda Suka Bata Mai Suna A Kotu
Ministan sadarwa na Najeriya Ali Isa Pantami ya mayar da martani ga kafafen yada labaran da suka wallafa rahoton cewa Amurka ta saka sunansa a jerin ‘yan ta’adda.

‘Yan Najeriya sun wayi garin a ranar Litinin da rahotanni a kafafen yada labarai na yanar gizo, wadanda suka ba wallafa cewa Amurka ta saka Pantami cikin jerin sunayen ‘yan ta’adda.

Sai dai cikin martanin da mayar a shafinsa Twitter @DrIsaPantami, ministan ya ce, kotu ce kadai za ta raba su da dukkan kafafen yada labaran da suka wallafa wannan labari.

“Duk manyan kafafen yada labaran da suka bata min suna, za su hadu da lauyoyina a kotu.” Pantami ya ce.

Ko da yake, kafar yada labarai ta NewsWireNGR wacce tana daya daga cikin wadanda suka wallafa labarin, ta ce ta janye rahotonta, amma Pantami ya ce, ta makara.

“@NewsWireNGR, na lura da janye labarin da kuka yi daga binciken da kuka gudanar, amma ka’idar bincike da aikin jarida ya tanada, ya bukaci a yi binciken ne kafin wallafa labarin ba bayan haka ba.” In ji Pantami

Muna dauke da karin bayan kan martanin da ministan ya mayar da abin da ‘yan Najeriya ke cewa.


Leave your vote

You may also like

Log In

Forgot password?

Forgot password?

Enter your account data and we will send you a link to reset your password.

Your password reset link appears to be invalid or expired.

Log in

Privacy Policy

Add to Collection

No Collections

Here you'll find all collections you've created before.

omg