Osinbajo:APC za ta ciro yan Najeriya miliyan 100 daga cikin talauci


Mataimakin shugaban kasa,Yemi Osinbajo ya ce jam’iyar APC za ta fito da yan Najeriya miliyan 100 daga cikin kangin talauci cikin shekaru goma masu zuwa.

A cewar kamfanin dillancin labaran Najeriya NAN, Osinbajo ya fadi haka a birnin Kebbi lokacin da ya kai wa mai martaba sarkin Gwandu, Muhammad Bashar ziyara.

Mataimakin shugaban kasar ya ce da hadin kan gwamnoni za a iya cika alkawarin da shugaban kasa Buhari ya yi na ciro yan Najeriya daga cikin kangin talauci.

Osinbajo ya ce yaje jihar ne domin taimakawa ƙananan sana’o’i wanda a cewarsa za su iya rage radadin talauci.

A cewarsa tsarin tallafawa masu kananan sana’o’i tsari ne da aka tsara domin bunkasa kasuwancin masu kananan sana’o’i.


Like it? Share with your friends!

1
83 shares, 1 point

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like