Osinbajo ya yi ganawar sirri da sarakunan Ogun kan matsalar rashin tsaro


Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya yi wata ganawar sirri a lokuta daban-daban da manyan sarakunan gargajiya biyu na jihar Ogun, Awujale na Ijebu, Oba Sikiru Adetona da kuma Akarigbo na kasar Remo, Oba Babatunde Ajayi.

Ganawar tasu na zuwa ne kwanaki kadan bayan da Ooni na Ife Oba Enitan Ogunwusi ya gana da shugaban kasa, Muhammad Buhari a fadar Aso Rock dake Abuja a akan matsalar tsaro da a ke fama da ita a yankin kudu maso yamma.

Osinbajo wanda ya fara ganawa da Akarigbo a fadarsa dake Sagamu ya tabbatar masa da kokarin gwamnatin tarayya na kawo karshen matsalolin tsaro da kasarnan take fuskanta.

Da yake magana jim kadan bayan ganawar ta su da Akarigbo ,Osinbajo ya ce shugaban kasa ne ya umurce shi ya gana da sarkin da kuma gwamnan jihar kan yadda za a inganta yanayin tsaro a yankin.


Like it? Share with your friends!

1

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like