Osinbajo ya jagoranci taron majalisar zartarwa ta tarayya


A ranar Litinin mataimakin shugaban kasa,Yemi Osinbajo ya jagoranci zaman majalisar zartarwar tarayya a fadar shugaban kasa dake Abuja.

Taron majalisar na ranar Litinin na daga cikin shirye-shiryen taron bankwana da aka shirya majalisar zata gudanar ranar Laraba.

Mataimakin shugaban kasar ne ke jagorantar zaman majalisar tun bayan da shugaban kasa, Muhammad Buhari ya tafi aikin umara kasar Saudiyya.

Buhari ya bar gida Najeriya ranar 16 fa watan Mayu inda ake sa ran dawowarsa Abuja ranar Talata 21 ga watan na Mayu.


Like it? Share with your friends!

1
75 shares, 1 point

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like