Osinbajo Ya Bada Tuta Ga Dan Takarar Gwamnan Gombe A Jam’iyyar APC Inuwa Yahaya


Dan takarar Gwamnan jihar Gombe a karkashin tutar Jam’iyyar APC a 2019, Alh. Muhammad Inuwa Yahaya, ya kaddamar da yak’in neman zabensa a yau Alhamis a karamar hukumar Kaltingo.

Toron ya samu halartar Sakataren Gwamnatin Tarraya Boss Mustapha, Gwamnan jihar Bauchi Barr. Abubakar Abdullahi Mohammed, Gwamnan jihar Adamawa Sen. Bindo Jibirin, Ministan muhalli Alh. Sulaiman Hassan Jara, Mataimakin Shugaban Jam’iyyar APC na shiyar arewa maso gabar Comr. Mustapha Silihu, Tsohon Gwamnan jihar Borno, Sen. Ali Madu Sharif, Da sauran Jami’an Gwamnatin tarraya, Harda Jiga-jigen Jam’iyyar na jiha, Dana shiyar Arewa maso gabar.

Jagoran Jam’iyyar APC na jihar Gombe, kuma Shugaban siyasar jihar Gombe, Sen. Dr. Mohammed Danjuma Goje, ya ce “mun hada karfi da karfe domin ceto jihar Gombe, lokaci muke jira na kafa Gwamnati da yardar Allah.

Allah ya kara mana yawan nasarori ya kaddara zaman Alh. Muhammad Inuwa Yahaya Gwamna a 2019,

Rahoton Abdul No Shaking

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like