Ooni na Ife yayi kira ga yan Najeriya su zabi wanda suke so a zabe mai zuwa


Adeyeye Enitan Ogunwusi,Ooni na Ife ya shawarci yan Najeriya da su zabi dan takarar da suke so ya zama shugaban kasarsu a zabe mai zuwa.

Basaraken yayi wannan maganar ne ranar Juma’a bayan da ya jagoranci sarakunan yankin kudu maso yamma inda suka kaiwa shugaban kasa Muhammad Buhari ziyara a fadar Aso Rock dake Abuja.

Da yake magana da manema labarai dake dauko rahoto daga fadar shugaban kasa ya ce ziyarar bata da alaka da siyasa face sun tattauna wasu batutuwan cigaba da suka shafi yankin kudu maso gabas.

“Saboda haka sakon mu ga kowa dake Najeriya dan Allah musamman matasan Najeriya kuje ku zabi duk wanda kuke so ku zaba,”ya ce.

Basaraken ya ce zabe ya gabato kuma ana cigaba da zaman d’ar-d’ar abu muhimmanci anan shine musan cewa Najeriya gaba take da kowannenmu.

Yakara da cewa sun zo fadar ne domin yabawa shugaban kasar kan kyawawan ayyukan da yake musamman kyakkyawar alakar dake tsakaninsa da mataimakinsa, Yemi Osinbajo wanda ya fito daga yankin.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like