Onnoghen zai san makomarsa ranar Alhamis


Kotun Da’ar Ma’aikata ta tsayar da ranar Alhamis a matsayin ranar da zata yanke hukuncin shari’ar da ake wa tsohon alkalin alkalan Najeriya, mai shari’a Walter Onnoghen.

Kotun na tuhumar Onnoghen da kin bayyana wasu kadarori da ya mallaka .

Alkalin kotun, Danladi Umar shine ya bayyana haka bayan da dukkanin bangarorin lauyoyin biyu suka kammala gabatar da hujjojinsu na tuhuma da kuma kariya.

Tun da fari,Okon Nkanu Effiong lauyan Onnoghen, ya yi kira ga kotun da tayi watsi da tuhumar da ake masa inda yace masu gabatar da kara sun gaza bayar da gamsassun hujjojin dake nuna ya aikata abin da ake tuhumarsa.


Like it? Share with your friends!

-1
58 shares, -1 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like