Ofishin jakadancin Afrika ta Kudu a Najeriya ya dakatar da ayyukansa


Ofishin jakadancin kasar Afrika ta Kudu dake Najeriya ya dakatar da ayyukansa.

Lunga Ngqenlele jami’i a ma’aikatar kasashen waje ta kasar ya fadawa kafar yada labarai ta ENCA dake kasar cewa an rufe ofishin ne na wucin gadi biyo bayan samun rahoton yinkurin kai hari kan ofishin.

Ngqengelele ya ce “Mun samu rahoto wasu mutane a Najeriya da Zambia sun yi kokarin kai hari kan wasu kamfanoni dake da alaka da Afrika ta Kudu a kasashensu,”

Jami’in ya kara da cewa kasar Afrika ta kudu na cigaba da tattaunawa da gwamnatin Najeriya kuma an tabbatar musu za a kare kadarori da kasuwanci dake da alaka da kasar ta Afrika ta Kudu.

Yan Najeriya da dama sabon rikicin kin jinin baki ya shafa a kasar Afrika ta Kudu.


Like it? Share with your friends!

1

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like