Obasanjo ya halarci taron gangamin jam’iyyar PDP a Abeokuta


Tsohon shugaban kasa,Cif Olusegun Obasanjo ya halarci taron gangami na daya daga cikin mai neman tsayawa takarar gwamnan jihar Ogun a karkashin jam’iyyar PDP,Oladipupo Adebutu.

Halartar taron da tsohon shugaban kasar ya yi ya jawo mutanen dake wajen taron sun rude da sowa.

Taron gangamin ya gudana ne a dakin karatu na Olusegun Obasanjo dake Abeokuta babban birnin jihar Ogun.

Da aka mika masa bututun magana Obasanjo ya yi wa jam’iyar da kuma dantakarar fatan samun nasara.

Obasanjo ya ce ya halarci wurin taron ne domin ka wai ya gaishe da mutane.

“Nazo wucewa ne shine na yanke shawarar tsayawa na ce muku barka dai, nayi muku fatan alheri ko wasa nake ko kuma dagaske nake za su sani. Na ganku anan kuma nazo na yi wasa daku,”Obasanjo ya fadawa Adebutu kafin ya nufi jerin gwanon motocinsa.

A shekarar 2014 ne tsohon shugaban ya keta katinsa na jam’iyar PDP a gaban yan jarida kuma tun wancan lokacin ne ya ce ya daina shiga jam’iyar siyasa.


Like it? Share with your friends!

1
84 shares, 1 point

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like