Obasanjo ya goyi bayan rufe kan iyakoki da Najeriya ta yi


Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya goyi bayan gwamnatin shugaban kasa, Muhammad Buhari kan matakin da ta dauka na rufe iyokinta inda ya shawarci makociyar Najeriya jamhuriyar Benin da ta sauya halayyarta.

Obasanjo ya bayyana haka ne ranar Talata yayin wani taron manema labarai a Addis Ababa babban birnin kasar Habasha, a wurin taro kan aiwatar da yarjejeniyar kasuwanci tsakanin kasashen Afrika.

Ya ce kaurin sunan da jamhuriyar Benin tayi wajen yiwa tattalin arzikin Najeriya zagon kasa ba abune sabo ba kuma Najeriya ta dade tana kawar da kai kan batun.

Obasanjo ya ce hakan yafaru lokacin da yake shugaban kasa inda ya kira shugaban kasar Benin na wancan lokacin domin su tattauna kan batun.

Ya kara da cewa yarjejeniyar kasuwanci ta kasashen ECOWAS ba an yi ta bane domin wata kasa ta kasance matattarar sauke kowanne irin kaya daga ƙasashen waje.

Matukar jamhuriyar Benin zata cigaba da kyale ana jibge kowane irin kaya domin shigar da su wasu kasashen to akwai matsala.


Like it? Share with your friends!

0

Comments 27

Your email address will not be published.

You may also like