Obasanjo ya gana da Atiku


Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo a ranar Alhamis ya gana da dantakarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a zaben shugaban kasa na ranar 23 ga watan Faburairu, Alhaji Atiku Abubakar, a Abeokuta babban birnin jihar Ogun.

Ganawar na zuwa ne kusan makonni uku bayan da Atiku yasha kayi a hannun shugaban kasa Muhammad Buhari na jam’iyyar APC.

Jaridar Daily Trust ta gano cewa, Atiku wanda ya yiwa Obasanjo mataimaki tsawon mulkinsa na shekaru 8 ya isa gidan tsohon shugaban kasar dake dakin karatu na Olusegun Obasanjo a birnin na Abeokuta.

Mai magana da yawun tsohon shugaban ƙasar , Kehinde Akinyemi ya tabbatar da ganawar.

“Abubakar ya iso da misalin karfe 12 na rana yayi ganawar sirri da Obasanjo suka kammala ganawar da misalin karfe 1 na rana daganan ya yi sallar Azahar kana yaci abincin rana kafin ya tafi.”

Comments 1

Your email address will not be published.

You may also like