Shugabanni da ma’aikatan hukumar kula da masu hidimtawa kasa da kuma masu hidimtawa kasa dake fadin kasarnan suna jimamin mutuwar masu hidimtawa kasa uku da suka rasa ransu a jihar Nassarawa.

A wata sanarwa da hukumar ta fitar tace  biyu daga cikin mamatan, Oguntola Wasiu da Danjuma Jamil Salihu sun mutu ne sakamakon nutsewa da suka yi a ruwa Assakio inda suka je wanka.

Daya marigayiyar Memunat Ahmad Yarwa ta mutune sakamakon matsala da ta fuskanta lokacin haihuwa.

A cewar sanarwa hukumar shirin “Yayi jimamin rasuwar wadannan gwarzaye musamman a wannan lokaci da suke bada gudunmawa wajen hadin kai da kuma cigaban kasa.

Za a ci-gaba da tunawa dasu kan kishin ƙasa rashin da kuma sadaukar da kai wajen hidimtawa kasa.”

Hukumar ta kuma sanar da sakin wata mai hidimtawa ƙasa, Nwankpa Blessing da aka yi garkuwa da ita a jihar Nassarawa.