Noman Shinkafa Ya Inganta A Jihar Kebbi


Kaf Nijeriya jihar Kebbi ta cirewa kowacce jiha hula a fannin noman shinakafa.

Hakan ya biyo bayan jajircewar Gwamna Atiku Bagudu ne, karkashin shugabancin shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari.

Idan muka dubi wadannan hotuna da kyau za mu ga shinkafa gata nan kamar a banza.

Wannan kasuwar shinkafa ce dake garin Yauri a jihar kebbi, daya daga cikin garuruwan mafi noman shinkafa a jihar Kebbi.

Jinjina zuwa ga Gwamnan jihar Kebbi, Alhaji Atiku Bagudu, da kuma shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Tabbas Gwamna Bagudu ya cancanci yabo dackuma jinjina bisa ga wannan aiki na habaka noman shinkafa.

Wani abun burgewa shine yanda ake daukar wannan shinkafa zuwa wasu jahohin Nijeriya, Musamman Legas, Yobe da sauransu.

Shinkafar ‘yar Kebbi da sauran jahohi ta toshe kasuwannin shinkafa irin su ‘yar Thailand da sauransu.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like