Nijeriya Za Ta Fara Sayen Man Fetur Daga Jamhuriyyar Nijar


Gwamnatin Nijeriya ta shiga sabuwar yarjejeniya da gwamnatin Jamhurriyar Nijar na fara shigo da man fetur daga birnin Zinder.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa Ministan arzikin man fetur na Najeriya, Temipre Sylva, da Ministan man jamhurriyar Nijar, Mr. Foumakoye Gado, ne suka rattafa hannu kan yarjejeniyar.

“Gwamnatin tarayyar Najeriya da Jamhurriyar Nijar ta rattafa hannu kan yarjejeniyar sufuri da ajiyar arzikin man fetur,” ma’aikatar arzikin mai a Najeriya ta bayyana a wani jawabi.

Bayan tattaunawa da aka kasance anayi tsakanin shugaba Muhammadu Buhari da shugaba Mahamdou Issoufou, na tsawon watanni hudu yanzu, kamfanin NNPC na Najeriya, da Societe Nigerienne De Petrole (SONIDEP), na Nijar sun amince da wannan harkalla.

Matatar man kasar Nijar Soraz dake Zinder, kimanin kilomita 260 da iyakan Najeriya, na da ikon tace kimanin gangan mai 20,000 a rana.

Gaba daya al’ummar kasar Nijar gangar mai 5000 a rana suke bukata, kuma suna da raran ganga 15,000 da suke bukatar sayarwa.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like