Nijeriya Tayi Asarar Dala Triliyan 1 Kan Biyan Haraji Gwamnatin Najeriya ta ce ta yi asarar kudin da ya kai Dala Triliyan guda a shekarar 2016 saboda yadda manyan kamfanonin kasashen waje da ke aiki a kasar suka ki biyan harajin da ya wajaba a kan su.

Mukaddashin shugaban Najeriya Ferfessa Yemi Osibanjo ne ya bayyana haka, inda ya ke cewar wannan ya sa gwamnatin ta shiga wasu yarjeniyoyi da kasashen duniya domin hana yadda kamfanonin ke kwashe kudaden zuwa kasashen duniya da zummar kaucewa biyan haraji.

Osibanjo ya ce gwamnati na daukan matakan da suka dace wajen ganin irin wadanan kamfanoni sun sauke nauyin da ke kan su wajen biyan harajin da ya wajaba.

Comments 0

Your email address will not be published.

Nijeriya Tayi Asarar Dala Triliyan 1 Kan Biyan Haraji 

log in

reset password

Back to
log in