Nijeriya Ba Matsiyaciyar Kasa Ba Ce, Ta Fada Hannun Matsiyata Ne A Baya – Masari


Gwamna Aminu Bello Masari ya bayyana cewa kasar nan ba matsiyaciya kasa ba ce, Amma ta fada hannun yan bani na iya ne kuma maras sa kishin ta, shi yasa muka fada cikin wannan hali da muka samu kanmu.

Masari ya fadi haka ne, a lokacin da yake jawabi a bikin cika Shekaru ashirin da biyar da kafuwar kwalejin Othman Fodio Katsina.

Masari ya cigaba da cewa idan kalli kasar nan ba manya mutane har sun mata yawa shugabannin ke babu. Wato shugaban da ke tafe ana bin shi Kuma Mai adalci, da tafiyar da alammurra kamar yadda Allah ya ce, amma manya mutane koina ga su nan. Shugabannin sune suka yi karanci.

Gwamna Masari ya kara da cewa maganar ilimi yana da muhimmanci sosai Kuma dole matasa su tashi tsaye su nemi shi da Kuma yin aiki da shi. Shi yasa wannan gwamnati ta tashi tsaye don ganin ta inganta harkar ilimi, daga tushe. Babban riga ko mukami ba yanci ba ne, ilimi shi ne yanci. Kuma hatta talauci a zucci yake, domin duk halin da ka ke ciki idan ka godewa Allah , Kuma zai Kara maka. Sai kaga mutum kamar bai iya cuta, Amma yana iya yinta, saboda cutar a cikin zuciya take Kuma ita ke halbin gangar jikin.

Daga karshi ya yi Kira ga malamai su tabbatar da gaskiyar abu kafin su hau munbari su yi waazi akai, saboda akwai yan kwalliya da addinin, su fadi karya don su burge mabiya. Ya Sha alwashin tallafawa makaranta domin ganin ta Kara samun cigaba Mai dorewa.

An karrama wasu daga cikin wadanda suka tallafawa makaranta tun daga kafuwarta Shekaru ashirin da biyar da suka wuce. Cikin su akwai Gwamna Aminu Bello Masari, Tsohan Gwamna farar hula na farko Allhaji Sa’idu Barda, Marigayi Abdu Haro Mashi, Alhaji Bilya Sanda, Abdullahi Garba Aminci.

Comments 1

Your email address will not be published.

You may also like