Ndume: Dalilin da ya sa za a cigaba da fama da rikicin Boko Haram a yankin arewa maso gabas


Ali Ndume, shugaban kwamitin majalisar dattawa kan harkokin sojoji ya ce za a cigaba da fama da matsalar yan tada kayar baya a yankin arewa maso gabas saboda karancin sojoji da kuma makamai.

Mayakan Boko Haram na cigaba da kai hari akan garuruwa dake yankin arewa maso gabas abin da ya tilastawa mutane da dama tserewa daga gidajensu.

Jihohin Borno da Adamawa sune inda rikicin ya fi yiwa mummunar illa.

Da yake magana da jaridar The Punch ranar Laraba, ya ce rikicin yan tada kayar bayan zai cigaba sai dai idan gwamnatin tarayya ta tura karin kayan yaki da kuma jami’an sojoji.

“Kalubalen da sojoji suke fuskanta a yanzu shine rashin kayan aiki da kuma isassun dakaru. Matukar ba a tura kayan aiki ba kamar yadda suke bukata to zamu cigaba da fama da kalubalen wannan ta’addancin.” Ya ce.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like