Jumullar mutane 180 da ake zargin manyan dillalan miyagun kwayoyi ne aka kama kan zargin mallakar fiye da kilogiram 3,331 na miyagun kwayoyi a jihar Nassarawa.

Kwamandan hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi, NDLEA a jihar, Sumaila Ethan, wanda  ya bayyana haka a wurin wani taron manema labarai a Lafiya.Ya ce manyan dillalai 47 aka yanke wa hukunci yayin da mutane 133 dake ta’ammali da miyagun kwayoyi aka bawa shawarwari bayan da aka warkar da su.

Ethan ya ce rundunar ta kama wani dillalin kwaya mai shekaru 40 , Godwin Okeke da aka samu da mallakar katan 118 na kwayar  Tiramadol da nauyin ta yakai kilogiram 2,873.88 a yankin Masaka dake karamar hukumar Karu ta jihar.

A cewar kwamandan an kama mutumin da ake zargin a  ranar 7 ga watan Disambar 2017.

Ethan ya bayyana cewa nau’in ƙwayar Tiramadol na daga cikin ƙwayar da aka fi amfani da ita a jihar.