Nazir sarkin waka ya sake gurfana a gaban kotu


Hukumar tace fina-finai ta jihar Kano, ta sake gurfanar da shararren mawakin nan, Nazir Ahmad wanda aka fi sani da sarkin waka a gaban kotun Nomans Land dake Kano.

An gurfanar da Naziru ne a kotun saboda zargin da ake masa na fitar da wakokin Gidan Sarauta da Sai Hakuri da yayi a ranar 12 ga watan Satumba na shekarar 2019

Bayan zaman kotun na yau an bayar da belin mawakin akan kudi naira miliyan 1 da kuma mutane 2 da zasu tsaya masa wanda dole daya daga cikinsu  ya zama dan uwansa sannan dayan ya zama kwamandan Hizbah a daya daga cikin kananan hukumomin jahar Kano.

Mutane da dama dai na zargin cewa ana yiwa mawakin bita da kulle saboda yadda yake nuna adawa da gwamnatin jihar ta, Abdullahi Umar Ganduje.


Like it? Share with your friends!

0

Comments 18

Your email address will not be published.

You may also like