Na’urar Card Reader guda 4695 gobara ta kone a Anambra


Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta kasa INEC ta bayyana cewa kiyasin farko da tayi kan gobarar da ta barke a wurin ajiye kayanta dake jihar Anambra ya nuna cewa na’urar tantance masu kada kuri’a wacce ake kira Card Reader a turance, guda 4695 ne suka kone.

Festus Okoye kwamishina a hukumar zabe ta kasa shine ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Talata.

Ya ce hukumar ta fara tattaro sauran na’urorin da suka yi ragowa a wasu jihohin domin tabbatar da cewa zaben ya gudana kamar yadda aka tsara.

Sanarwar ta bayyana cewa karo na uku kenan irin wannan gobarar na faruwa biyo bayan makamanciyarta da ta faru a ofisoshin hukumar dake kananan hukumomin Isiala Ngwa da kuma Qua’an dake jihohin Abia da kuma Plataeu.

Tuni dai jam’iyar adawa ta PDP ta tsargi jam’iyar APC da hannu a tashin gobarar.

Jam’iyar ta PDP ta ce bayanan sirrin dake gabanta sun nuna cewa jam’iyyar APC ce ke haddasa gobarar a wuraren da take ganin PDP nada magoya baya da yawa.


Like it? Share with your friends!

1
73 shares, 1 point

Comments 1

Your email address will not be published.

You may also like