NANS Ta Gana Da Sheikh Gumi Kan Yadda Za A Ceto Daliban Da Aka SaceKungiyar daliban jami’o’in Najeriya NANS, ta kai wa Sheikh Ahmad Gumi ziyara a jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin kasar.

Wata sanarwa da shugaban kungiyar Sunday Asefon ya wallafa a ranar Litinin ta ce, tawagar daliban ta tattauna da Shehin malamin kan al’amuran da suka shafi kare lafiyar daliban Najeriya a duk jami’o’i da kuma matakan da za a bi don sako wadanda aka yi garkuwa da su.

“Mun yi magana kan yadda za a ci gaba da tattaunawa dangane da yadda za a sako daliban da aka sace da kuma matakan da ya kamata a bi wajen ganin an tabbatar da cewa makarantu suna da cikakken tsaro.

Shugaban NANS, Sunday Asefon (hagu) da Sheikh Gumi (dama) (Facebook/NANS)

Shugaban NANS, Sunday Asefon (hagu) da Sheikh Gumi (dama) (Facebook/NANS)

“Saboda dalibanmu su gujewa fargabar yiwuwar a yi garkuwa da su.” Asefon ya ce.

“Za mu ci gaba da tattaunawa da masu ruwa da tsaki don tabbatar da tsaro a makarantu.” Shugaban na NANS ya ce.

A ‘yan watannin baya Sheikh Gumi, ya kan shiga daji don ya yi wa ‘yan fashin dajin wa’azi tare da sauraren korafe-korafensu.

A baya-bayan nan ‘yan bindigar sun sace dalibai da malamai a kwajelin kimiyya da fasaha ta Nuhu Bamalli da ke garin Zaria.

Kazalika sun sace dalibai sama da 100 a wata makarantar Islamiyya da ke garin Tegina a jihar Neja.

Sannan sun yi garkuwa da daliban sakandaren gwamnatin tarayya da ke Yawuri a jihar Zamfara.

Har yanzu ba a jin duriyar dukkan wadannan dalibai da aka sace.

‘Yan bindigar kan nemi a biya su miliyoyin kudade kafin su saki mutanen da suka yi garkuwa da.

Hukumomi a matakin jiha da tarayya sun ce suna iya bakin kokarinsu wajen ganin sun magance matsalar tsaron musamman wacce ta shafi satar mutane don neman kudin fansa.


Leave your vote

You may also like

Log In

Forgot password?

Forgot password?

Enter your account data and we will send you a link to reset your password.

Your password reset link appears to be invalid or expired.

Log in

Privacy Policy

Add to Collection

No Collections

Here you'll find all collections you've created before.