Nan Da Wani Dan Lokaci Kadan Za Mu Kawo Karshen Matsalar Tsaro A Nijeriya – Sabon Shugaban Hafsoshin Tsaron Na Kasa, Janar Leo IraborSabon shugaban hedikwatar tsaro, Manjo Janar Leo Irabor ya bada tabbacin cewa nan gaba kadan matsalar tsaro za ta zo karshe a Nijeriya.

Majo Janar Irabor ya bayar da wannan tabbaci ne jim kadan bayan ganawar da yayi da sauran shugabannin sabbin tsaron Nijeriya tare da shugaban kasa, Muhammadu Buhari.

Manjo Janar Irabor ya ce shugaba Buhari ya ba su umarnin kawo ci gaba a harkar tsaro sannan kuma sun san cewa akwai tunanin zasu kawo canji dake zukatan mutane dan hakan ne ma za su dage wajan ganin sun yi iya bakin kokarinsu.

Muna rokon Allah Ya baiwa sabbin Hafsoshin tsaron Nijeriya nasara akan ‘yan ta’addan Nijeriya.


Like it? Share with your friends!

-2

Comments 10

You may also like