Nan Da Kankanin Lokaci Shugaba Buhari Zai Dawo Gida Najeriya – Gwamna Yahaya Bello Gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello ya ba yan Najeriya tabbacin cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari zai dawo kasar nan ba da dadewa ba daga hutun jinya da ya tafi birnin Landan.

Gwamna Bello ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a 16 ga watan Yuni lokacin da ya jagoranci manyan ‘yan Najeriya gurin addu’adon samun lafiyar shugaban kasar.

Gwamnan ya bayyana cewa shugaban kasa Buhari zai dawo nan kusa domin ya ci gaba da kyawawan ayyuka na gyara kasar.

Vanguard ta rahoto cewa an gudanar da addu’o’in ne a lokacin sallar Juma’a a masallacin gidan gwamnati a Lokoja, babban birnin jihar Kogi.

Daya daga cikin wadanda suka halarci taron shine tsohon gwamnan jihar Kano Sanata Kabiru Gaya.

A baya mun shaida muku cewa gwamnatin jihar Sokoto ta kashe kimanin naira miliyan 91 don daukar nauyin malaman musulunci zuwa kasar Saudiya don yin aikin Umurah da yiwa shugaba Buhari addu’ar neman lafiya

Da yake magana a ranar Talata, 13 ga watan Yuni, kwamishinan kula da harkokin musulunci na jihar Sakkwato, Alhaji Mani Katami ya bukaci malaman da zasu tafi umuran da suyi ma shugaban kasa Muhammadu Buhari addu’ar samun lafiya.

Comments 0

Your email address will not be published.

Nan Da Kankanin Lokaci Shugaba Buhari Zai Dawo Gida Najeriya – Gwamna Yahaya Bello 

log in

reset password

Back to
log in