Najeriya zata sayo karin jiragen yaki daga Rasha


Najeriya za ta sayi makamai da suka hada da jiragen yaki masu saukar ungulu daga kasar Rasha domin kara daura damara a yakin da take da mayakan Boko Haram da kuma yan bindiga da suke dauke da makamai.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Mallam Garba Shehu shine ya fadi haka lokacin da yake ganawa da manema labarai a fadar shugaban kasa dake Abuja.

Shehu ya ce Buhari zai gana da shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin kan sha’anin tsaro a wurin taron kasar Rasha da Nahiyar Afirka da zai gudana a birnin Sochi.

Har ila yau ganawar shugabannin biyu za ta mai da hankali kan sauran bangarori da suka da makamashi da kuma kasuwanci.


Like it? Share with your friends!

0

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like