Najeriya za ta ruguje idan aka zabi Buhari – Peter Obi


Peter Obi, dan takaran kujeran mataimakin shugaban kasa karkashin jam’iyyar PDP, yace idan aka kuskura aka zabi shugaba Muhammadu Buhari, Najeriya za ta ruguje.

Jaridar PUNCH ce ta hakaito wannan jawabi ne yayinda yake magana da manema labarai a kan titin Awka, babban birnin jihar Anambara.
Yace gwamnatin APC ba tada karfin mulki saboda haka jama’a su kawa da wannan gwamnati a zabe mai zuwa.

Yace: “Muna kamfen kan titi domin aika saknmu ga yan Najeriya. Muna fada musu cewa wannan zaben na rana goben yaranmu ne.”

“Muna samun karfin gwiwa da irin goyon bayan da muke samu a ko ina, ba a kudu maso gabas kadai ba saboda mutane sun ga gaskiyan al’amari.”

“Sun gani cewa wannan gwamnati ba tada karfi da salon mulkin Najeriya.”

“Sun gano cewa idan aka kuskura aka bari Buhari ya cigaba kasar nan za ta ruguje. Tun da mun kawo kasar na rugujewa, wajibi ne kowa ya mara mana baya.”

“Mun ga yadda rashin tsaro ke kara yawa kulli yaumin. Mun tashi daga na bakwai zuwa na uku cikin kasashe marasa zaman lafiya bayan kasar Afghanistan da Iraqi. Wannan abin damuwa ne. “


Like it? Share with your friends!

1
71 shares, 1 point

Comments 1

Your email address will not be published.

You may also like