Najeriya za ta kasance kasa ta biyu a duniya da ta fi shigo da shinkafa


Ma’aikatar noma ta Amurka ta yi hasashen cewa Najeriya za ta kasance kasa ta biyu a fadin duniya da tafi sayan shinkafa daga kasashen waje.

Hasashen ya nuna cewa kasar China za ta kasance kasa ta farko da za tafi shigar da shinkafa cikin kasar daga ƙasashen waje.

“China da Najeriya za su cigaba da kasancewa wadanda suka fi shigo da shinkafa a shekarar 2019 ya yin da Tarayyar Turai ke bi musu baya sai kuma kasashen Cote di’ voire da Iran .”a cewar hasashen.

Tun da fari ministan harkokin noma na Najeriya, Audu Ogbeh ya yi gargadin cewa kasar na iya fuskantar karancin shinkafa a shekarar 2019 idan har ba a dauki matakai ba biyo bayan ambaliyar ruwa da aka samu a wasu jihohin.

Gwamnatin shugaban kasa, Muhammad Buhari ta ci alwashin kawo karshen dogaro da kasashen waje da Najeriya ta yi wajen samun shinkafar da take bukata


Like it? Share with your friends!

2
119 shares, 2 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like