Najeriya za ta kara samun kudin shiga idan aka soma hako mai a Arewa – Diran Fawibe


Wani babban Masanin harkar tattalin arziki a Najeriya kuma shugaban kamfanin Dr Diran Fawibe a wata hira da yayi da da jaridar Daily Trust yayi bayani a game da hako fetur da ake yi a Arewa.

Diran Fawibe ya bayyana cewa akwai bukatar a hako fetur din da ke Arewacin Najeriya, Masanin yace wannan zai ba gwamnatin Najeriya kudin shiga, kuma zai taimakawa masu kananan matatun danyen man fetur a cikin kasar.

Dr. Fawibe yake cewa ya kamata ace Najeriya tayi nisa da fara aiki da man da ke kwance a Arewacin kasar kamar yadda sauran kasashen Duniya su ke yi. Masanin ya dai nuna cewa hako man Arewa zai taimaki Najeriya kwarai.

Bayan nan kuma wannan babban Masani yace ana sa rai kamfanin tace danyen man fetur da Aliko Dangote yake ginawa ya kammalu kwanan nan. Diran Fawibe yace samuwar wannan kamfani ba zai kashe sauran matatun kasar ba.

Wannan kwararren Masanin ya nuna cewa sha’anin tace man fetur yana da matukar wahala, har ya fi hako man fetur zama jan-aiki.

A wannan hira mai tsawo da yayi da ‘yan jarida, yace kayyade farashin kayan mai bai da amfani.

Shugaban kamfanin na International Energy Services (IES), Fawibe, ya kuma bayyana cewa akwai bukatar shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake duba kudirin nan na PIB da ake tunani zai gyara sha’anin man fetur a Najeriya.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like