Najeriya Ta Sayo Jirgin Yakin Ruwa Bayan Shekara 41
Rundunar sojin ruwa ta Najeriya, na shirin kaddamar da wani sabon jirgin yakin ruwa wanda za a yi a kasar Hadaddiyar Daular Larabawa.

A cewar mai baiwa Shugaba Buhari shawara kan sha’anin kafafen sada zumunta na zamani, Bashir Ahmad, za a kaddamar da jirgin ne a wata mai Yuni.

“Za a kaddamar da shi ne a Sharjah na kasar Hadaddiyar Daular Larabawa a wata mai zuwa.”

Jirgin yana da tsawon mita 100 wanda zai rika daukan makaman yaki.

“Wannan babban ci gaba ne, lokacin na karshe da Najeriya ta kaddamar da irin wannan jirgi (wanda ake kira LST a takaice,) tun a 1979 – shekara 41 kenan.”

Jiragen ruwan na LST, akan yi amfani ne da su ne wajen dakon makaman yaki kamar tankuna da rokoki wadanda akan tsallaka da su daga wani yankin zuwa wani.

Dadin dadawa, jiragen yakin sama kan iya sauka akansu.

A kwanan hukumomin Najeriyar sun bayyana cewa, sun yi cefanan wasu jirage yakin sama daga Amurka, wadanda su ma ake shirin kawo su nan ba da jimawa ba.

Najeriya na fama da matsalolin tsaro da suka hada da na Boko Haram a arewa maso gabashi da ‘yan fashin daji a arewaci maso yammaci, da kuma mayakan haramtacciyar kungiyar IPOB mai fafutukar kafa kasar Biafra a kudu maso gabashi.


Leave your vote

You may also like

Log In

Forgot password?

Forgot password?

Enter your account data and we will send you a link to reset your password.

Your password reset link appears to be invalid or expired.

Log in

Privacy Policy

Add to Collection

No Collections

Here you'll find all collections you've created before.