Najeriya ta sayo jiragen saman yaki marasa matuki


Rundunar sojan saman Najeriya ta sayi jiragen yaki marasa matuka guda biyu daga kasar China.

Jiragen yakin marasa matuki da ake kira WingLoong II za a yi amfani da su ne wajen yaki da yan ta’addar Boko Haram da kuma yan bindiga da suka addabi wasu sassa na kasar nan.

Mai magana da yawun rundunar sojan saman, Ibikunle Daramola shi ne ya sanar da sayen jiragen cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter.

Daramola ya ce yanzu Najeriya ta bi sawun kasashen Hadaddiyar Daular Larabawa, China da su ne ka dai su ke amfani da irin wannan jirage.

Ya kara da cewa cikin shekara me zuwa ne za a sake karo wasu ƙarin jirage marasa matuka guda shida.


Like it? Share with your friends!

-2

Comments 47

You may also like