Najeriya ta rushe a hannun Buhari -Secondus


Uche Secondus shugaban jam’iyyar PDP ya ce Najeriya ta rushe karkashin mulkin Buhari.

A wata tattaunawa da ya yi da Jaridar Punch, Secondus ya yi mamakin dalilin gwamnatin tarayya na dora alhakin kashe-kashen da suke faruwa cikin kasarnan akan yan siyasa.

Shugaban na PDP ya zargi gwamnati da barin ainihin abin da yake faruwa inda take karkatar da hankulan mutane daga gaskiya.

“Akwai wani abu da ba dai-dai ba, shiyasa nake kiran hukumomin kasa da kasa da su gudanar bincike saboda su baza su nuna san rai ba. Tunda gwamnatin tarayya ta fara dora alhakin kashe-kashen dake faruwa akan yan siyasa,”ya ce.

“Wannan ce dai gwamnatin da ta ce masu kashe-kashen daga Libiya su ke kuma wani bangarene na kungiyar Boko Haram amma kuma yanzu suka canza maganar su. Suna cewa yan siyasa ne fulani makiyaya wannan ka wai wani shiri ne na yiwa yan siyasa sharri domin a kama su a kulle sun yi haka ma ga yan jam’iyar su da ra’ayinsu bai zo daya ba.

“Suna yin haka akan mu, sun kyale ainihin gaskiyar abinda ke faruwa suna karkatar da hankulan mutane daga gaskiya.Wannan kasar ta rushe a hannun shugaban kasa Muhammad Buhari.”


Like it? Share with your friends!

3
82 shares, 3 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like