Hukumomi sun ce allurai 4,080,000 na allurar rigakafin cutar Moderna da gwamnatin Amurka ta bayar za a rarraba wa ‘yan kasa a makwanni masu zuwa.

Ndaeyo Iwot, babbar sakatariyar hukumar kula da lafiya a Abuja ta ce “Muna matukar fatan za mu biya bukatun mafi yawan mutanen da suka yi ta kira.” “Ku tuna har yanzu muna sa ran ƙarin allurar AstraZeneca, da ma na Johnson da Johnson, suna nan tafe, wannan labari ne mai daɗi a gare mu.”

Hukumomin Najeriya na burin yin allurar rigakafin kashi 40 cikin 100 na yawan jama’arta, ko kuma mutane miliyan 80, zuwa karshen wannan shekarar da kuma karin kashi 30 cikin 100 a karshen shekarar 2022.

Amma hukumomi sun ce abu ne mai wahala a samu rigakafin cutar saboda abin da suka kira mako daga kasashe masu arziki.

“Yana da mahimmanci ga kowace ƙasa ta sami damar yin allurar rigakafin COVID-19 idan za mu iya kawar da COVID-19,” in ji Faisal Shuab, babban darekta a Hukumar Ci gaban Kiwon Lafiya ta ƙasa. “Yana da mahimmanci cewa akwai madaidaicin damar yin allurar rigakafin ta yadda a matsayin al’umma ɗaya ta duniya za mu iya kawar da COVID-19.”

Najeriya, kamar sauran ƙasashe, a halin yanzu tana fama da hauhawa cutar coronavirus da mummunar nau’in Delta ke haifarwa.

A watan Maris, Najeriya ta samu kusan allurai miliyan hudu na allurar AstraZeneca ta hannun cibiyar COVAX da WHO ke tallafawa, wani shirin agaji na duniya wanda ke neman tabbatar da samun allurar rigakafin cutar a duniya.

A watan da ya gabata, ‘yan majalisar dokokin Najeriya suka amince da wasu dala biliyan 2.4 a cikin karin kudade don taimakawa gwamnati ta sayo rigakafin COVID-19, da kayan aiki ga sojoji.