Najeriya ta doke Benin da ci 2 : 1


Najeriya ta fara wasa da kafar dama a wasan neman cancantar shiga gasar cin Kofin Nahiyar Afirka na shekarar 2021, bayan da ta doke jamhuriyar Benin da ci biyu da daya.

An buga wasan ne a filin wasa na Godswill Akpabio dake Uyo babban birnin jihar Akwa Ibom.

Yan wasan kasar Benin ne suka fara zurawa kungiyar Super Eagle kwallo daya a raga mintuna kadan da fara wasan ta hannun, Stepahane Sessegnon wanda ya yi hanzarin amfani da damar kuskuren da yan bayan Najeriya suka yi.

Victor Osimhen shine ya zurawa Super Eagle kwallon farko ta bugun daga kai sai mai tsaron gida mintuna kadan kafin a tafi hutun rabin lokaci.

Bayan da dawowa hutun rabin lokaci, Samuel Kalu ya kara kwallo daya a ragar jamhuriyyar Benin inda aka tashi wasan Najeriya 2 : Benin 1.

A ranar Lahadi tawagar ta Najeriya zata kara da kasar Lesotho.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like