Najeriya ta dade da kasancewa babbar abokiyar huldar kasuwanci da kasar Girka, wanda kuma ake ganin zai iya dorewa da karfafa ne kawai idan kasashen biyu suka kara maida hankali wajen kawancen kasuwanci da sauran nau’o’in tattalin arziki.

Wannan ya fito ne a lokacin wani babban taron shekara-shekara na farko akan karfafa dangataka tsakanin kasashen biyu, wanda hukumar nan ta kawancen Najeriya da Girka (BWG) ta gudanar a Abuja.

Daya shugaban hukumar Ambasada Samson Itegboje, ya fada a wajen taron cewa, Babban bankin samar da ci gaba na kasar Girka da hukumar karfafa sana’o’i ta kasar, sun ba da tallafin kudade a lokuta da dama domin karfafa kasuwanci a Najeriya.

Babban taron Dangantakar Najeriya da kasar Girka a Abuja

Babban taron Dangantakar Najeriya da kasar Girka a Abuja

Haka kuma ya ce hukumomin sun bude kofofinsu ga masana’antu na Najeriya a haujin aikin gona da fasahar noma ta zamani, kimiyya da ayukan kiwon lafiya, karfafawa matasa da koyon sana’o’i da kuma fasahar sadarwa ta zamani.

Itegboje ya ce kasashen biyu sun amince da shirin kawancen bunkasa iraruwan noma, fitar da kayayyaki da kuma musayar ilimi da bincike a tsakanin su.

To sai dai Najeriya ta jaddada bukatar kara adadin yawan jama’ar da za su ci gajiyar kawancen, da tabbatar da raba-daidai a tsakanin jinsi da yankuna, a yayin aiwatar da ayukan samar da ci gaba na kasar ta Girka a Najeriya.

Manyan jami’an da suka halarci taron sun hada da jakadan kasar Girka a Najeriya Harry Dijk, Babban Sakatare a ma’aikatar harkokin wajen Najeriya Ambasada Gabriel Aduda, da kuma takwaransa na ma’aikatar cinikin da lamurran saka jari ta najeriya Dr Nasir Sani-Gwarzo, da sauransu.