Najeriya bata bukatar sanatoci 109 da yan majalisar wakilai 360


Rochas Okorocha, sanata dake wakiltar mazabar yammacin Imo ya ce Najeriya bata bukatar sanatoci 109 da kuma yan majalisar wakilai 360.

Da yake magana ya yin zaman majalisar na ranar Alhamis,Okorocha ya ce ya kamata a rage yawan yan majalisun daga kowace jiha domin rage kudin da ake kashewa wajen tafiyar da gwamnati.

Ya ce yawan sanatoci daga kowace jiha, ya kamata a rage ya koma daya, ya yin da kowace jiha za ta zama tana da yan majalisar wakilai uku kacal.

“Me sanatoci uku suke da sanata daya ba zai iya yi ba?” Okorocha ya tambaya.

Okorocha ya ce bai san wani abu da majalisar dattawan ta keyi a yanzu da za a ce ya banbanta dana majalisar dattawan da ta gabace ta karkashin Bukola Saraki.


Like it? Share with your friends!

0

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like