Najeriya ba ta da niyar yanke huldar da Afrika ta Kudu -Onyeama


Geoffrey Onyeama, ministan harkokin wajen Najeriya ya ce kasar baza ta yanke huldar jakadanci da kasar Afrika ta Kudu saboda harin da aka kai wa yan Najeriya mazauna kasar.

Ya fadi haka lokacin da ya bayyana gaban kwamitin majalisar dattawa kan kasashen waje.

Ministan ya ce yan Najeriya mazauna kasar baza su zo a dauki wannan mataki ba.

Ya ce Najeriya za ta duba wasu karin hanyoyin bayan difilomasiyya domin warware rikicin da yake faruwa.

Ya kuma bayyana cewa wakili na musamman da shugaban kasa Buhari ya tura kasar zai dawo Najeriya ranar Asabar.

A karshe ya ce gwamnatin na daukan matakan da suka da ce kan harin na baya bayan nan da aka kai kan Najeriya.


Like it? Share with your friends!

-1
81 shares, -1 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like