Najeriya ba ta bukutar Majalisar dattawa – Fayemi


Gwaman jihar Ekiti, Kayode Fayemi ya ce Najeriya za ta iya soke majalisar dattawa saboda kasar za ta iya dogara da majalisa guda daya kacal wato majalisar wakilai.

Gwamnan yayi wannan furucin ne a wurin taro na musamman game da tattalin arzikin Najeriya karo na 25 wanda aka gudanar a Abuja.

Fayemi ya ce: “Akwai bukatar gwamnatin Najeriya ta duba fadinta, ni ina goyon bayan tsarin majalisa guda daya kacal wadda ita ce majalisar wakilai saboda su ke wakiltarmu.”

“Jihar Ekiti na da sanatoci uku haka ita ma jihar Legas sanatoci uku ne da ita duk da kuwa bambancin girman jihohin. A ganina babu adalci cikin lamarin, zai fi kyau idan gwamnati ta soke majalisar dattawan gaba daya. Saboda akwai abubuwa masu muhimmanci da yawa da gwamnatin za ta iya yi.” Inji Fayemi.

Idan baku manta ba dai majalisar dattawa na dauke ne da sanatoci 109 yayin da majalisar wakilai ke cike da mambobi 360 daga jihohin Najeriya 36.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like