Gwamnatin jihar Filato ta sanya dokar hana zirga zirgar jama’a a tsakanin  wasu kananan hukumomi uku na jihar, sakamakon tashin hankali da ya auku a ranar Asabar.

Yankunan da dokar ta shafa dai su ne; Jos ta Arewa da Bassa da kuma Jos ta kudu. Dokar za kuma ta fara aiki ne daga karfe shida na yammaci zuwa karfe shida na safiya.

Wata sanarwa da gwamnan jihar Filato Simon Lalong ya sanya wa hannu, ta ce an dauki matakin ne sakamakon yadda hankulan al’umma suka tashi bayan kisan wasu matafiya Musulmai akalla 30 a Safiyar Asabar yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa kudancin Najeriya.

Sanarwa ta gwamnatin jiha ta Filato ta ce jamai’an tsaro na kokari wajen ganin an zakulo wadanda ke da hannu wajen aikata kisan, sannan ta yi Allah wadai da irin halin da jihar Filato ta shiga na bakin ciki saboda faruwar lamarin.