Daga cikin makiyayan da aka kashe sun hada da mata tara da kananan yara shida da maza uku da kuma wani magidanci daya, wadanda maharan suka bi su har rugarsu suka kuma yi musu harbin kan mai uwa da wabi a yankin Oyi da ke jihar Anambra.

Yankin na kudancin Najeriya da ‘yan kwanakin nan rikicin masu rajin ballewa daga kasar ke ta karuwa, sai dai har ya zuwa wannan lokacin babu wata kungiya da ta fito ta dauki alhakin wannan aika-aikar.

Najeriya da ke da mafi yawan al’umma a nahiyar Afirka na kuma da sama da kabilu 250 wanda dangantaka a tsakanin wasu kabilun ke kara tsami a baya-bayan nan.