Na Yi Wa Almajirai 32 Luwadi A Makarantar Allo, Inji Abdullahi Abubakar


Rundunar ‘yan sandar Jihar Neja ta cika hannu da wani mutum mai suna Abdullahi Abubakar da ake zargi da yi wa almajirai 32 luwadi a karamar hukumar Kontagora dake Jihar ta Neja.

Abubakar wanda ke daya daga cikin masu kula da almajiran ya amsa cewar lallai yana shiga dakin da almajiran ke kwana cikin dare yana luwadi da su ba tare da sanin su ba.

Kwamandan Hisba na karamar hukumar Kontagora Malam Murtala Abdullahi (Zan Wuce) ne ya gabatar da karar ga ofishin ‘yan sanda na “A” division Kontagora bayan samun koke da korafe-korafe na cututtuka a duburar almajiran ba tare da sanin abunda ya jawo masu ciwon ba. Bayan samun koken ne, DPO ‘yan sandan mai kula da “A” division Kontagora CSP Muhammad Umar Dakingari cikin gaugawa ya tura jami’an sa inda suka kamo wanda ake zargin.

Da yake zantawa da manema labarai a lokacin da rundunar ta gabatar da shi ga ‘yan Jarida wanda ake zargin Abubakar ya amsa laifin sa nayin luwadi da almajiran, inda ya ce a cikin dare yake shiga dakunan da almajiran ke kwana yana tube masu wanduna yana yin luwadi dasu.

“Ina yin luwadi da almajiran kullum ba tare da sanin sauran malammai da shugabannin makarantar ba-Inji shi.

Abubakar wanda ya bayyana wannan mummunar al’amari da cewar aikin shedan ne, ya kara da cewar yayi lalata da almajirai kimanin talatin da biyu, ba zan iya fayyace yadda na fara wannan al’amari ba kawai aikin shedan ne, kuma ina cike da nadamar aikata hakan.

Kakakin randunar ‘yan sandar Jihar ta Neja Muhammad Abubakar ya bayyana cewar faruwar wannan mummunar al’amari ya kara nuna irin yadda almajiran ke fuskantar cin zarafi a wasu makarantun allo. Ya kara da cewar rundunar ta su na cigaba da gudanar da kwakkwaran bincike domin zakulo sauran masu aikata irin wannan cin zarafi da mummunar aika aika ga almajirai a cikin Jihar Neja.

Abubakar Muhammad yasha alwashin rundunar ‘yan sandar zata kawo karshen cin zarafi da lalata da almajirai a makarantun allo, kuma zasu zakulo duk masu labewa da karatun allo suna aikata miyagun aiyuka.


Like it? Share with your friends!

2
93 shares, 2 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like