Na kamu da cutar mura saboda ina aiki tukuru, a cewar Buhari


Shugaban kasa, Muhammad Buhari ya ce yana fama da cutar mura ne sakamakon aiki tukuru da yake yi.

Buhari ya fadi haka ne lokacin da yake gabatar da kasafin kudin shekarar 2020 gaban yan majalisun tarayya.

Buhari ya bayyana cewa ya kamu da murar saboda aiki tukuru da yake domin ganin bai saba lokacin da majalisun suka saka masa ba na gabatar da kasafin.

Ya roki yan majalisun da kuma sauran bakin da suke zauren majalisar da suyi masa afuwa saboda muryarsa tana rawa.

“Kamar yadda kukeji.Ina mura sakamakon aiki tukuru wajan ganin cika wa’adin da kuka saka mini,” ya fada cikin raha.

A jawabinsa shugaban majalisar wakilai,Femi Gbajabiamila ya jajantawa shugaban kasar kan murar da take damunsa.


Like it? Share with your friends!

-1
76 shares, -1 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like