Mutumin da ya kafa kungiyar OPC ya mutu


Fredrick Fasehun,wanda ya kafa kungiyar yarabawa zalla ta OPC ya mutu.

Jaridar Punch ta rawaito cewa Fasehun ya mutu da safiyar ranar Asabar a asibitin koyarwa na jami’ar jihar Lagos dake Ikeja.

Rahotonni sun nuna cewa an kwantar da Fasehun a sashen kulawa da marasa lafiya dake cikin mawuyacin hali a ranar Talata inda ya cigaba da kwanciya a sashen har ya zuwa lokacin mutuwar sa.

“Gaskiya ne Baba ya mutu da safiyar yau a dakin da ake lura da marasa lafiya dake cikin mawuyacin hali na jami’ar jihar Lagos dake Ikeja”a cewar Adeoye Jolaosho mai magana da yawun marigayin.

Ya yin da mutane da dama dake yankin kudu maso yamma ke kallon Fasehun a matsayin wani gwarzo abin koyi a yankin arewa kuwa lamarin ya sha bamban,mutane da dama na ganin marigayi a matsayin wanda ya taka rawa wajen kashe yan arewacin kasar a rikicin kabilanci da yafaru a yankin kudu maso yamma.

Comments 1

Your email address will not be published.

  1. Ko yarbawa su Kira Shi gwarzo ko mene ne ma dai yan AREWA Sun sha gabansa
    kuma yanzu ya tarar da abin da ya aikata, ko mene aka ambace Shi da suna

You may also like