Mutum guda ya mutu a hatsarin jirgin kasa da ya faru a Lagos


Mutum guda aka tabbatar da mutuwarsa wasu da dama kuma suka jikkata a wani hatsarin jirgin kasa da ya faru da safiyar yau Alhamis a jihar Lagos.

Hatsarin ya faru ne lokacin da biyu daga cikin taragwon jirgin suka jirkite akan hanyar Mongoro- Agege dake birnin na Lagos.

Manajan lardin Lagos na Hukumar Kula Da Jiragen ƙasa ta Najeriya, Injiniya Jerry Oche ya tabbatar da mutuwar.

Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 07:15 na safe lokacin da jirgin dake makare da mutane ya kauce daga kan digarsa.

Binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa jirgin ya kauce ne sakamakon rashin kyawun hanya.


Like it? Share with your friends!

1
89 shares, 1 point

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like