Mutum daya ya mutu yayin da wata kwantena ta fado kan mota a Lagos


Wani mutum guda ya rasa ransa bayan da wata kwantena ta fado kan wata karamar mota a jihar Lagos.

Mummunan lamarin yafaru ne ranar Asabar akan titin Mobolaji Bank Anthony dake Ikeja.

Wata babbar mota ce ke dauke da kwantenar mai tsawon kafa 20.

Shugaban hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Lagos LASEMA, Adesina Tiamiyu wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce kwantenar ta fado kan motar inda ta danne mutanen dake ciki.

Ya ce mutumin ya mutu ne kafin a kawo musu dauki.

Jami’an hukumar sun dauke gawar tare da motar da motar.

Hatsari irin wannan abune da yake yawan faruwa a birnin Lagos kuma hukumomi sun gaza shawo kan lamarin.


Like it? Share with your friends!

-1
83 shares, -1 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like