Mutanen da na sani ne ka dai zan nada ministoci -Buhari


Shugaban kasa Muhammad Buhari ya ce ba zai kara zaben mutanen da bai sani ba domin su zama ministoci.A wani taro karo na farko da ya gudanar da shugabannin majalisar kasa ya ce mutanen da aka taba gwadawa ne kawai kuma za su iya yin aikin da aka basu, su ne za su shiga cikin jerin sabbin ministocin da zai naɗa.A wurin taron da ya gudana a babban dakin taro dake fadar shugaban kasa da daren ranar Alhamis, Buhari ya ce yana fuskantar matsin lamba akan ya kafa majalisar zartarwa ta tarayya.Ya ce duk da matsin lambar da yake fuskanta mutane masu gaskiya ne kadai za a nada muƙamin minista.Shugaban kasar ya koka cewa a baya mutanen da ya nada ministoci wasu mutane da kuma jami’ya ta mika masa sunayensu.


Like it? Share with your friends!

0

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like