Mutane uku sun kone kurmus a gobarar tankar mai a jihar Ogun


Mutanen da basu gaza uku ne ba aka bada rahoton sun mutu a yayin da wasu da dama suka jikkata bayan da wata tankar mai ta kama da wuta a Abeokuta babban birnin jihar Ogun a ranar Talata.

Haka kuma motoci biyar ne da kuma babura biyu suka kone a gobarar tankar man.

Shugaban hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Ogun, Ige Olufalorin ya ce mutanen da gobarar ta rutsa da su sun kone kurmus baza a iya gane su ba.

Wasu da suka sheda faruwar lamarin sun ce motar tankar ce ta kwace lokacin da take sakkowa daga wata gada inda ta kade wani me babur dake tafiya kafin ta cikaro da wasu motoci dake jiran daukar fasinja.


Like it? Share with your friends!

0

Comments 2

You may also like