Mutane sama da 20 sun mutu a gobarar da ta kama a kamfanin sayar da iskar gas a jihar Delta


Wata gobara da ta tashi a masana’antar sayar da iskar gas ta kashe mutane sama da 20.

Lamarin ya faru ne a wurin sayar da gas na Osadebe Gas Plant dake garin Agbor hedkwatar karamar hukumar Ika ta kudu a jihar Delta.

Gobarar da da ta faru ranar Juma’a ta kuma bar wasu mutane da dama da raunukan kuna dake barazana ga rayuwarsu.

Wutar da ta kama a masana’antar ta bazu ya zuwa gidajen dake makotaka da wurin.

An garzaya da mutanen da lamarin ya rutsa da su ya zuwa cibiyar kula da lafiya ta tarayya dake Asaba da kuma asibitin koyarwa na jam’iar Benin.


Like it? Share with your friends!

1

You may also like