Mutane da dama ne suka mutu bayan da wata babbar mota tayi cikin kasuwa a jihar Ekiti


Aƙalla mutane sama da ashirin aka rawaito sun rasa rayukansu a wani hatsarin mota da yafaru a jihar Ekiti.

Hatsarin yafaru ne ranar Lahadi da daddare bayan da wata babbar mota dake dauke da shinkafa ta kwace tayi cikin kasuwa.

Rahotonni sun nuna cewa motar ta kwace ne baya da direbanta ya yi kokarin ta ka birki amma ya shanye.

Direban ya yi kokarin tsayar da motar ta hanyar hadata da ginin gefen titi amma ta kwace tayi cikin kasuwar.

Mutanen da ke cikin kasuwar sun kaure da koke da kuma alhinin rashin da suka yi.

Motar na kan hanyarta ta zuwa jihar Ondo dauke da shinkafar wani sanata da ake tunanin cewa ya saya ne domin rabawa magoya bayansa.

Akasarin yan siyasa na amfani da irin wadannan kayayyaki wajen bawa magoya bayansu dama masu kada kuri’a.


Like it? Share with your friends!

-1
103 shares, -1 points

Comments 1

Your email address will not be published.

You may also like