Mutane 77 sun mutu a girgizar da aka yi a kasar Indonesia


Hukumar dake kare afkuwar bala’o’i a kasar Indonesiya ta ce akalla mutane 77 ne gsuka mutu a wata girgizar kasa da aka yi a lardin Sulawasi dake yammacin kasar.

Sama da mutane 820 ne suka jikkata a yayin da wasu 15,000 suka tsere daga gidajensu bayan girgizar kasar mai karfin 6.2.

Girgizar kasar ta lalata gidaje sama da 400 da wasu otal guda biyu ta kuma rusa baki dayan wani asibiti da kuma ofishin gwamnan yankin.

Kasar Indonesiya ta kasance kasa da ake yawan samu afkuwar girgizar kasa.


Like it? Share with your friends!

0

Comments 1

You may also like