Mutane 73 aka kashe tare da kona ƙauyuka 50 a sabon rikicin da ya barke a jihar Taraba


Aƙalla mutane 73 aka kashe tare da kona wasu ƙauyuka 50 biyo bayan sabon rikicin da ya barke tsakanin Fulani da kuma al’ummar Yandang dake karamar hukumar Lau ta jihar Taraba.

Sahabi Mahmud, shugaban kungiyar Miyetti Allaha a jihar ya fadawa yan jaridu ranar Juma’a cewa ya’yan kungiyar 23 aka kashe a rikicin.

Ya ce sama da mutane 3000 da yawancinsu yara da mata da rikicin ya raba da gidajensu yanzu suna samun mafaka a sakatariyar kungiyar majalisar musulmai dake Jalingo da kuma sauran makotan ƙananan hukumomi.

Anasa ɓangaren wani mai fada aji a al’ummar Yandang, Aaron Artimas, ya ce sama da mutane 50 a bangaren Yandang da kuma sauran kabilu dake a yankin aka tabbatar sun mutu a rikicin.

Artimas ya ce shekaru aru-aru kabilun Fulani, Yandang, Mumuye da Yoti da kuma sauran kabilu suna rayuwa a yankin cikin zaman lafiya ba tare da rikici ba.

Ya dora alhakin tashe-tashen hankulan da suke yawan faruwa a yanzu kan wasu mutane daga waje wadanda suke so a rika damawa da su a siyasance.


Like it? Share with your friends!

-1

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like